YANDA BLOCKCHAIN YAKE AIKI

 Yanda Blockchain Yake Aiki:


Zanyi wannan rubutun ne saboda abin da yake faruwa da TON Blockchain chikin kwanaki biyun nan, har zuwa yanzu da nake wannan rubutun. Sannan zanyi misali da bankuna domin saukaka fahimta.


Bari mu fara da gwari-gwari: Misali, ace dukkanin bankunan da muke dasu a Nijeriya kowannensu blockchain ne, kamar ace GTBank shine Ethereum blockchain, Zenith Bank shine Solana, UBA shine Tron, Access Bank shine BSC, da sauransu. Kuma dai mun sani cewa blockchain yana zama chikakkene idan ya hada wasu manyan diraku (pillars) uku, wato DECENTRALISATION, SECURITY da SCALABILITY. Kenan, zamu iya cewa dukkanin bankunan (blockchains) din nan dole ya kasance sun hada wayannan dirakun (pillars).


Bari mu dauki daya daga chikin wayannan dirakun, wato SCALABILITY. Scalability a blockchain yana nufin saurin tura transaction. Ma'ana, idan muka koma kan bankunan chan (blockchains), scalability dinsu yana nufin yanda suke saurin tura kudi daga banki zuwa banki. Misali, kowanne banki yanada yanayin saurinsa, wani bankin idan mutum ya tura kudi dashi, chikin yan sakwanni kudin zasujewa wanda ya tura, wani bankin chikin yan mintuna, wani bankin kuma har anganesu da matsalar jinkiri wajen tura kudi. Harma idan ka bawa wani account number din bankin domin ya tura maka kudi, sai kaji ya tambayeka, shin baka da wani bankin? Domin yasan bankin yanada matsala wajen amsar kudi ko turawa. Wannan shine ake kira da scalability a blockchain.


Saurin tura kudi ya danganta da karfin banki (blockchains), yanayin saurin tura kudin kuma shine ake kira da TRANSACTIONS PER SECOND (TPS) a blockchain. Misali, wani bankin (blockchain) zai iya tura transactions dubu goma (10,000) chikin second daya, kenan za'ace yanada karfin 10,000 TPS. Kowanne banki (blockchain) yanada karfin TPS dinsa, ma'ana idan aka wuce wannan TPS din nasa, to zai samu matsala. Misali, idan bankin mai suna A (bari muce TON blockchain) yanada 10,000 TPS, hakan na nufin mutane 10,000 zasu iya tura transactions lokachi guda kuma dukkansu kudin yajewa wayanda aka turawa chikin second daya (one second), to yaya zata kasance kuma idan mutane maliyan daya (1M) suka tura transactions lokachi guda, yayinda karfin TPS dinsa kuma 10,000 ne?


Tun daga ranar da akayi launching na $DOGS, TON blockchain yayi nauyi sosai, nauyin da yasa tura assets (token) akansa yake daukar dogon lokachi baije inda aka turashi ba. Hakan yasa ake ganin akwai babban qalubale akan TON blockchain na rashin daya daga chikin diraku uku da kowanne blockchain ya kamata ace yana dasu, wato SCALABILITY. Ma'ana, karfin transaction per second (TPS) dinsa.


Rashin scalability akan blockchain ba karamar barazana bace gareshi, domin yakansa fargaba azuchiyoyin investors da developers (builders). Saboda manyan projects zasuji tsoron gina ko dora projects dinsu akansa, saboda gudun jinkiri yayin tura transactions. Rashin scalability shine yake sawa kuga an kirkiri blockchain amma team dinsa na tsoron bada dama a dora masa tokens akansa, saboda gudun bayyana gazawarsu.


Ana gane karfin blockchain ne daga lokachin da aka fara samarda protocols da dora masa tokens akansa. Akwai tokens samada 50,000 akan Ethereum, akwai dubunnai akan Solana, hakama akan BSC, kuma dukda hakan suna sunada karfin TPS, don haka idan aka tura assets akansu ba'a samu delay, chikin yan sekwanni yaje. Idan launching na DOGS mai mutane 42M zai tsayar da Ton blockchain, ya zata kasance kenan idan Hamstar, TapSwap, da sauransu sukayi launching nasu?


Ya kuke tunanin zata kasance aduniyar blockchain da ace Solana ko Ethereum ne suka samu wannan tangardar ta scalability? 


Akwai aiki sosai akan TON blockchain team.



Comments

Popular posts from this blog

SIRRIN JALABI MAI KARFI

YADDA AKE HADA MAGANIN KARIN GIRMAN NONO

MAGANIN TOILET INFECTION